Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Bacewa Jirgin Saman Gwamnatin Nijar Ya Yi?


Tsohon jirgin gwamnatin Nijar da ake zargin ya bace
Tsohon jirgin gwamnatin Nijar da ake zargin ya bace

Jirgin saman gwamnatin Nijar da aka saya shekaru 40 da suka gabata, da ake zaton ya bace ne yana wurin gyara a Ingila kuma yayinsa ya wuce saboda haka mahukumtan kasar ke tunanen sayar dashi, matakin da ‘yan adawa suke kushewa

Shekaru kusan hudu ke nan da ‘yan kasar Nijar suka daina jin duriyar jirgin sama safuring boeing 747 da mahukuntan kasar ke anfani dashi.

Rashin ganin jirgin ya sa jama’ar kasar suna shakkun inda yake dalili ke nan da ‘yan adawa suka bukaci gwamnatin kasar ta fitar da jama’a daga duhu.

A bayanan da ya bayar a zauren majalisar dokokin kasar ministan tsaron kasa Kalla Mukhatari ya sanar cewa gangaci ne na ‘yan adawa da suka yi zargin bacewar jirgin. A cewarsa shekaru 40 da suka wuce aka sayi jirgin. Yanzu yana Ingila wurin gyara.

An kiyasta cewa kudin jirgin zai kai kimanin miliyan dari biyar na sefa amma yana bukatar miliyan dubu biyu na sefa domin a yi masa gyaran da yake bukata. To sai dai an gano cewa duniya ta daina yayin irin jirgin saboda haka masana suka shawarci gwamnatin kasar ta yi gwanjonsa.

Hukumomin kasar Nijar sun ce zasu sayar da jirgin ga mai so saboda babu yadda za’a yi dashi a wannan zamanin.

Amma kakakin ‘yan majalisar dokoki na bangaren adawa Sumaila Sanda wanda shi ya bukaci sanin inda jirgin yake na ganin rashin dacewar sayar dashi saboda ya yiwa kasar aiki.

Souley Barma nada karin bayani a rahotonsa

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG