Duk da yanayin talaucin da wasu ke ganin ya taimaka wajen sa iyaye suna tura ‘ya’yansu kananan yara cikin halin barace-barace da sunan neman ilimi, yanzu an soma samun makarantun allo wadanda dalibansu basu fita yawon bara.
Malamai da shugabannin al'umma sun nuna bukatar karfafa wannan tsarin domin kawar da matsalolin da baran kan jefa al'umma ciki.
Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar, ta bakin Wazirin Sakkwato farfesa Sambo Wali Junaid, ya ce wannan tsarin na neman ilimi ba tare da yara sun yi bara ba ya dace a karfafa irinsa a kowace al'umma.
Alal misali, a karkashin shirin gwamnatin jihar Sakkwato na inganta harkar almajiranci, jagoran shirin kuma Sakataren Zartaswa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin musulunci, Dr Umar Altine Dandin Mahe ya ce yanzu haka an tantance makarantun allo fiye da dubu biyu a Sakkwato daga cikin su an samu 38 wadanda suka dogara da kansu, almajiransu basu yawon barace-barace, hakan ne yasa ake kara musu kwarin gwiwa.
Masana sun yi hasashen cewa idan wannan tsarin na makarantun allo ya tsayu da kafafuwansa akwai yuwuwar kwararowar almajirai daga jihohin da suka yanke shawarar korarsu, abinda kan iya kawo cunkusonsu a Sakkwato ta yadda watakila tsarin zai iya samun tangarda idan sauran wurare ba su aiwatar da shi, amma daya daga cikin yan kwamitin kula da wannan tsarin.
Ofishin asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Shiyyar Sakkwato na cikin masu ra'ayin talauci ya taimaka ga yawaitar wancen tsari na almajiranci, amma jami'ar ofishin, Safiy Tahir Abdullahi ta ce akwai alamun samun nasara a tsarin.
Ga Muhammad Nasir da cikakken rahoton:
Facebook Forum