Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN MURYAR AMURKA: Amurka Na Maraba Lale Da Kafa Sabuwar Gwamnati a Somaliya


Sabon Firaministan Somaliya, Hamza Abdi Barre
Sabon Firaministan Somaliya, Hamza Abdi Barre

Amurka ta taya Somaliya murnar kafa sabuwar gwamnati tare da yi ma ta tayin yin aiki tare don amfanar kasashen biyu.

Amurka na taya Somaliya murnar kafa gwamnatinta, kuma tana fatan yin aiki tare da ita domin tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta, in ji Ambassador Richard Mills, Mataimakin wakilin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya. Kalubalen da Somaliya ke fuskanta sun hada da sulhunta gwamnatin kasa da mambobi na tarayya, da kammala nazarin kundin tsarin mulkin tarayya, da kuma samun nasarar yafe ma ta basussuka.

Barazanar kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabaab ta na cigaba da zama babbar abin damuwa, kamar yadda wani mummunan harin da aka kai ranar 20 ga watan Agusta ya nuna a otal din Hyatt da ke Mogadishu. Ambasada Mills "ya yi matukar Allah wadai da wannan harin" kuma ya ce "Amurka na ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa kokarin da Somaliya ke yi na fatattakar al-Shabaab:"

“Muna taya jami’an tsaron kasar Somaliya murna saboda nasarar da suka samu ta fatattakar al-Shabaab daga yankin Hiran. . . Mun himmatu wajen yin amfani da kayan aikin da ake da su don yakar ta'addanci, ciki har da bayar da tallafi kai tsaye ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta (AU) a Somaliya da kuma jami'an tsaron Somaliya, da kuma yin amfani da rukunin takunkuma wajen751 da aka ware ma Somaliya, don ayyana 'yan ta'addar al-Shabaab da ke ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a Somaliya da ma Gabashin Afrika baki daya. Muna kira ga sauran kasashe mambobin kungiyar da su yi hakan.”

A matsayinta na mai ba da agaji mafi girma a Somaliya, Amurka ta ci gaba da jajircewa wajen yin wani abu kan fari da ba a taba ganin irinsa ba wanda ya shafi sama da mutane miliyan bakwai da ke fuskantar karancin abinci.

Gargadin baya-bayan nan cewa ana hasashen za a yi yunwa a wata mai zuwa, yekuwa ce ta neman dukkanninmu mu dau mataki, in ji Ambassador Mills. Yunwa, in ji shi, kalubale ne da babu wata kasa da za ta iya magancewa ita kadai:

“Dole ne kasashen duniya su dauki matakin bai daya, tare da sadaukar da duk abubuwan da ake bukata don dakile karuwar asarar rayuka da abubuwan zaman gari . . . .Gwamnatin Amurka ta bayar da taimakon sama da dala miliyan 700 ga kasar Somaliya a bana a daidai lokacin da ta ke fama da farin da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya kunshi sama da kashi 70 cikin 100 na duk gudunmawar da shirin ba da agajin jin kai na MDD ya bayar a Somaliya. Muna kira ga sauran abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa su faɗaɗa gudunmawar su don agajin jin kai."

Amurka tana matukar goyon bayan al'ummar Somaliya kuma tana ci gaba da jajircewa wajen yin aiki tare da ita don ciyar da dimokiradiyya gaba da kuma ci gaban kasashen biyu.

Wannan shi ne sharhin Muryar Amurka, mai bayyana ra’ayin Gwamnatin Amurka.

XS
SM
MD
LG