Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shaidu Sun Ce Jiragen Sama Sun Kashe Mutane da Dama a Yankin Tigray na Habasha


Harin jirgin sama a Tigray
Harin jirgin sama a Tigray

Mutane da dama sun mutu a wani harin jirgin sama a ranar Talata a garin Tagogon da ke yankin Tigray a Habasha, a cewar shaidu.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce wani jirgin sama ne ya jefa bam a kasuwar yankin da misalin karfe 1 na rana.

Ma’aikatan lafiya sun ce sojojin Habasha sun hana motocin daukar marasa lafiya isa wurin da harin ya faru. Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ce wani mai magana da yawun sojojin Habasha, Kanar Getnet Adane, ya yi magana a kaikace game da zargin.

Kanal din bai tabbatar ko musanta harin ba, yana mai cewa kawai hare-hare ta sama dabarun soja ne na yau da kullun kuma sojoji ba sa kai hari kan fararen hula.

A ranar Talata, mazauna sun ce sabon fada ya barke a ‘yan kwanakin nan a arewacin babban birnin Tigray, Mekelle.

Yankin na Tigray dai ya dade ya na cikin rikici tun daga watan Nuwamba, lokacin da sojojin Habasha suka kaddamar da farmaki domin fatattakar ‘Yan tawayen Jam’iyyar ta Tigray mai mulki ko kuma Tigray People's Liberation Front (TPLF) . Sojojin Eritiriya suna taimakawa sojojin Habasha wajen yakar kungiyar ta TPLF a rikicin da ke faruwa.

Tun lokacin da fadan ya barke, an kashe dubban mutane yayin da wasu kimanin miliyan 2 suka tsere daga gidajensu don gujewa tashin hankalin.

XS
SM
MD
LG