Shaidu a kasar Ivory Coast ko Cote D’Ivoire, sun ce an girka sojoji masu yin biyayya ga Laurent Gbagbo a kusa da hotel din da abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara, ya mayar hedkwatarsa. Jami’ai na kusa da Ouattara sun ce an yi harbe-harbe a yau litinin a lokacin da tsoffin ‘yan tawaye dake gadin Mr. Ouattara a cikin Gold Hotel na Abidjan suka tinkari sojojin na Gbagbo. Ba a samu rahoton jin rauni ba, haka kuma jami’;an sun ce ba a san ko su wanene suka yi harbe-harben ba. An bada rahoton cewa sojojin na Gbagbo sun toshe wata hanya ta zuwa hotel din. Mr. Gbagbo da Mr. Ouattara duk su na ikirarin samun nasara a zaben shugaban kasa da aka yi kwanakin baya, kuma kowannensu ya kafa ta sa gwamnatin. Amma kuma akasarin kasashe da cibiyoyin duniya sun ce Mr. Ouattara ne ya lashe zaben, kuma su na matsawa Gbagbo lamba a kan ya sauka ya bar masa gadon mulki. Yau litinin a birnin Brussels, ministocin harkokin wajen Kungiyar Tarayyar turai sun kafa takunkumin kudi da na tafiye-tafiye a kan Mr. Gbagbo da mukarrabansa, su na masu fadin cewa za su ci gaba da aiki da takunkumin har sai ya sauka ya bar ma Ouattara kujerar mulki.
Shaidu a Ivory Cost sun ce an girke sojojin dake biyayya ga Laurent Gbagbo kusa da otel din da Allasane Quattara ya mayar shelkwata
Shaidu a Ivory Cost sun ce an girke sojojin dake biyayya ga Laurent Gbagbo kusa da otel din da Allasane Quattara ya mayar shelkwata.