A jiya Litinin 9 ga watan Maris 2020, majalisar zartarwa ta jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje, ta sauke mai martaba Malam Muhammed Sanusi II, a matsayin Sarkin Kano na 14.
Saukewar ta biyo bayan rashin jituwa tsakanin gwamnar jihar Ganduje da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, inda aka zarge shi da rashin mutunta dokoki da al'adun jihar Kano.
Mai martaba Malam Muhammed Sanusi II, ba shine sarkin gargajiya na farko da aka taba saukewa daga karagar mulki ba a Najeriya. An sauke dimbin sarakunan gargajiya daga mukaminsu saboda dalilai daban-daban.
An sauke kakan Mai Martaba Muhammed Sanusi na daya, daga gadon mulki a shekarar 1963 da aka zarge shi da nuna rashin bin doka ga hukumomin siyasa. An sauke shi ne bayan ya shafe shekaru tara yana gadon mulki.
Mai martaba Umar Tukur, Sarkin Muri, sarkin gargajiya a Arewancin Najeriya, shi kuma an sauke shi saboda ana zargin ya ki bin dokokin gwamnan jihar.
Muri tana karkashin tsohuwar jihar Gongola, wanda a lokacin take karkashin mulkin Yohana Madaki. Madaki ya zargi mai martaba sarkin da rashin aikata ba daidai ba a cikin fada.
Daga baya an raba jihar zuwa jihohin Adamawa da Taraba a shekarar 1991.
Mai martaba Sultan Ibrahim Dasuki, Sarkin Musulmi, wanda aka sauke shi a lokacin gwamnatin mulkin soja, saboda ya ki bin dokokin gwamnatin wannan lokacin. An sauke shi a shekarar 1996 kuma aka kore shi daga jihar.
Haka kuma ko a shekarar 2005 gwamnatin siyasa karkashin jagorancin Alh. Adamu Aliero, ta sauke Mai Martaba Sarkin Gwandu Alh. Mustapha Haruna Jokolo, mai murabus, wanda ya taba zama dogarin shugaban milkin soja Janar Muhammadu Buhari, wanda shima aka zarge shi da rashin da’a ga gwamnatin jiha.
Amma baya ga wadannan sarakunan Arewacin Najeriya, a sauran sassan kasar, an sauke sarakuna daban-daban sakamakon rashin biyayya.
Akwai sarakuna kamar, sarkin Benin (Oba of Benin), Oba Ovoramwen Nogbaisi, da Alaafin Oyo, Adeyemi Adeniran II.
Facebook Forum