Yayin da kungiyoyi da daidaikun jama’a a fadin duniya ke kokarin dakile sauyin yanayi, ita ma hukumar sojin Najeriya ba a bar ta a bay aba. Da yak e magana a wani taron manema labarai a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Shugaban Shashin Tsare-tsare na Rundunar Sojin Ruwan najeriya Admiral Johnson Olutoyin y ace sauyin yanayi, musamman wanda kan faru haka kwatsam, na da hadari ga tsaron kasa musamman ta cikin ruwa da tattalin arziki da kuma cigaban kasa baki daya.
Ya ce a kokarinta na yakar wadanda matsalolin, rundunar sojin Najeriya ta himmatu ga yaki da barayin danyar mai da ‘yan ta’adda da safarar kwayoyi.
Wani kwararre kan sauyin yanayi y ace lallai al’amarin na tasiri kan ayyukan soji musamman ma na ruwa. Y ace muddun yanayi ya canza sai ya shafi yadda sojojin ruwan ke kai koma cikin ruwa da kuma yadda su ka san sannan ruwan.
Ga wakilinmu Hassan Maina Kaina da rahoton: