Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauya halaye na taimakawa wajen rage kamuwa da cutar kanjamau


Wani mai fama da cutar kanjamau
Wani mai fama da cutar kanjamau

Wani fitaccen likita a Amurka ya karfafa bukatar sauya hali a matsayin hanyar yaki da cutar kanjamau.

Wani fitaccen likitan yaki da cututuka a Amurka Dr. Daniel Halperin yana karfafa kwararru na kasa da kasa a fannin aikin lafiya, su karfafa bukatar sauya hali a matsayin muhimmiyar hanyar da zata taimaka wajen yaki da cutar kanjamau.

Likitan ya bayyana haka ne a cikin wani littafi da suka rubuta na hadin guiwa tare da Craig Timberg, wani tsohon editan jaridar Washington Post.

A cikin littafin mai suna “Tinderbox: How the West Sparked the AIDS Epidemic and How The World Can Finally Overcome it.”, marubutan sun bayyana yadda yin kaciya a wadansu kasashen nahiyar Afrika ya taimaka wajen rage yada cutar kanjamau.

Banda kaciya kuma, suka ce, an sami raguwar yada cutar kanjamau a kasashe da dama da suka hada da Uganda da kuma Zimbabwe, da dadewa kafin a sami magunguna da suke rage kaifin cutar.

A cikin gangamin da gwamnatin shugaba Yoweri Museveni na kasar Uganda tayi, kimanin shekaru 20 da suka shige, an fadakar da jama’a su guji cutar su kuma ji tausayin iyalan da zasu bari a baya. Yayinda aka kuma yi kira ga maza da mata su rage yawan mutanen da suke jima’i da su.

Marubuta littafin sun ce sauya halin rayuwa da kuma yiwa maza kaciya sun fi arha fiye da sauran hanyoyin yaki da cutar kanjamau kuma suna ta tushe a al’adun jama’a.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG