Miliyoyin al’umar musulmi ne suka gudanar da Sallah a masallatan idi daban daban kimani dari dake sassan birnin Kano, da kewaye.
Dr. Muhammadu Sani Ayagi, wanda ya jagoranci Sallar Eid Fitr, a masallaci harabar tsohuwar jami’ar Bayero dake Kano, baya ga tambihi akan bukatar al’umar Musulmi suyi riko da darussan da suka koya a Ramadan, Malamin ya hori ‘yan siyasa dasu yi la’akari da maslahar al’uma a yayinda da suke fafutukar cimma muradunsu na kama madafun iko.
Ya kara da cewa al’umar Musulmi siyasa ta dade tana yiwa al’umar Musulmi illa saboda haka yace ya zama wajibi a dauke son zuciya domin daukar abinda Allah yake so.
A jawabansu na Sallah Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, sun nanata mahimmancin hadin kai tsakanin al’umomi daban daban da suke zaune a jihar Kano.
Facebook Forum