Janarar Irabor wanda ke magana yayin da yake marabtar Babban hafsan hafsoshin rundunare tsaro na kasar Sao tome and Principe Janar Idalecio Pachire a Ofishinsa dake Abuja inda suka tattauna batun kalubalen tsaro a gabar tekun Guinea da irin rawar da kasashen biyu ke takawa.
Babban hafsan mayakan Najeriyar ya sha alwashin ci gaba da tunkarar matsalar fashin teku da sauran nau'o'in aika aika a cikin ruwan gabar tekun Guinea
Sauran hanyoyin da kuma sojojin kasashen biyu zasu maida hankali shine wajen Horas da dakarun kasar Sao Tome, Atisayen hadin gwiwa da sojojin Najeriya da sauran nau'o'in tallafi ga rundunar sojin kasar ta Sao Tome.
Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar mayakan kasar Sao Tomen Janar Pachire kazalika ya ziyarci hedkwatar sojojin ruwan NAJERIYA da hukumar tattara bayanan sirri ta rundunar tsaron Najeriya
Najeriya da Sao Tome dai sun dade suna da tarihin kyakkyawar alakar Diflomasiyya da na sha'anin tsaro da ya dauki she karu masu yawa.