ACCRA, GHANA, Tsohon basaraken gargajiyan ya bayyana haka ne wata hira da ‘yan jarida a Accra babban birnin kasar Ghana. Ya ce, kasashen da suka ci gaba, kamar su Amurka, China, Ingila da sauran kasashen da suke da arzikin masana’antu, su ne suka yi wa yanayi illa, ba kasashen Afirka ba.“Kuma mu Afirka, mu ne za mu sha wahalar abin saboda ba mu shiryawa yadda za mu kare kan mu ba. Kamar yadda muke da rana, ya kamata a shigo da kudi yadda za a gina harkar lantarki ta amfani da sola”, domin kasashen Afirka babu kudi da masaniyar yadda za a gina hakan.
Kasashen na Afirka na ci gaba da fama da illolin sauyin yanayi, duk da cewa gudummawarsu ga illar yanayi ba ta taka kara ta karya ba, idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya, musamman masu arzikin masana’antun.
Rahoton Binciken Majalisar Dinkin Duniya na cewa, Afirka na fitar da kashi 2 zuwa 3 cikin 100 ne kawai na hayakin Carbon da ake fitarwa a duniya, amma Afirka ce ke samun karuwar zafin rana na kusan 0.7 na ma’aunin Celsius, fiye da yawancin Nahiyoyin, tare da hasashen cewa, yanayin zafi zai karu; za a sa mu karuwar fari da kuma ambaliyar ruwa.
Hasken rana yana taimakawa wajen rage yawan iskar carbon da sauran iskar gas da ake fitarwa zuwa sararin samaniya, kuma zai iya maye gurbin kusan kashi 80 cikin 100 na makamashin da ake bukata.
Sanusi II ya kara jaddada cewa, magance matsalar sauyin yanayi na tafiya ne da kare al’umma da tattalin arzikin kasa, kuma kasashen da suka fi kawo illa ga yanayi su ya fi dacewa da ba da tallafin kudi wajen ba da makamashin hasken rana, domin yadda yake da muhimmanci a kare muhalli haka kuma yake da muhimmanci a kare rayuwar al’umma.
Mohammed Jafaru Dankwabia, Mataimakin darektan bincike na cibiyar canjin yanayi da tsaron abinci (CCCFD), ya jaddada muhimmancin makamashin hasken rana. Ya ce, makamashin harken rana shi ne na biyu wajen samun sarrafaffen makashi a duniya, kuma gina shi ya fi saukin kudi fiye da sauran makamashi, kamar na fetir, kwal da gas.
Masana sun bayyana cewa, zuba hannun jari a makamashin hasken rana a Afirka, baya ga samar da tushen makamashi mai dorewa, zai taimaka ga tattalin arziki. Zai samar da ayyukan yi; zai inganta samar da wutar lantarki; zai kuma kara habaka tattalin arziki, wanda zai haifar da kyakkyawar makoma da wadata ga Nahiyar Afirka.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah:
Dandalin Mu Tattauna