Yace a matsayinsu na 'yan majalisa su ne kundun tsarin kasa ya baiwa ikon tantance abun da aka gabatar masu kafin su amince.
A cewarsa bisa ga tsarin mulki duk abun da suka zartas babu inda za'a ce sun wuce gona da iri, ko basu bi ka'ida cikin abun da suka yi.
Karin da suka yi da ake cecekuce akai yanzu ya samo asali ne daga gyaran da Majalisa tayi bisa kan tsarin kasa na kashe kudi nan da shekaru uku. A cikin wannan ne suka dauko na wannan shekarar suka saka cikin kasafin kudin da aka gabatar masu. Baicin haka sun kara farashin mai da Naira biyu wanda ya bada zarafin karin.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum