WASHINGTON, DC —
Alkalumma da aka tara sun nuna cewa cikin watanni uku da suka gabata kimanin mutane 250,000 suka rasa muhallansu a jihohin Yobe da Borno da Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya sanadiyar rikicin kungiyar Boko Haram.
A cewar hukumar dake bada agajin gaggawa ta Najeriya ko NEMA a takaice, sashen arewa maso gabas daga watan Janairu na wannan shekarar zuwa wannan watan mutane dubu dari biyu da hamsin suka rasa muhallansu a jihohin Borno, Yobe da Adamawa. Alhaji Muhammed Kanar jami'in dake kula da hukumar a yankin arewa maso gabas ya yi karin haske.
Yace a jihar Borno lamarin ya rutsa da mutane fiye da miliyan daya da dubu dari uku. A jihar Adamawa fiye da mutane miliyan daya yawancinsu mata da yara da tsofaffi rikicin ya rutsa da su. Haka ma a Jihar Yobe inda aka kashe daliban kwalajin Buni Yadi rikicin ya rutsa da mutane fiye da dubu dari bakwai da saba'in.
Ita hukumar NEMA tace ta samu alkalumman ne sanadiyar aikin hadin gwiwa da tayi tare da kungiyar bada agaji ta Red Cross da kuma hukumomin bada agaji na jihohin da abun ya shafa. Binciken da hukumomin suka gudanar ya nuna cewa a yanzu haka yawancin mutane a arewa maso gabas basa iya cin abinci sau uku a rana daya.
Amma Alhaji Muhammed Kanar jami'in NEMA yace suna iyakacin kokarinsu wurin tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Yace kokarin da suke yi yanzu shi ne su tabbatar sun kai abinci a duk wuraren da basu da abinci musamman a jihar Borno. Yace duk gidajen da aka kona an kona ne da sutura da abinci. Bayan an tanadi abinci Alhaji Kanar yace za'a zo a yi kokarin sake ginawa mutane gidajensu. Amma babbar matsala yanzu ita ce ta rashin abinci idan kuma babu abinci mutane ba zasu dawo cikin hankalinsu ba.
Matsalar da hukumar ta fi fuskanta yanzu ita ce ta tsaro. Wasu wurare da suke son su je rashin tsaro ya kawo masu cikas. Kamata yayi a ce kawo yanzu sun gama kai agajin abinci a duk jihohin uku sun kuma fara aikin gyara gidaje. Wurin da yakamata su je cikin kwana daya sai ya daukesu sati daya ko biyu basu samu sun je ba.
Ga rahoto.