Shekaru biyu da kirkiro da ma'aikatar samar ma matasa aikin yi a jihar Gombe da nufin an rage munanan dabi'u tsakanin matasa a jihar, musamman dabi'ar nan ta kalare wadda ta sa jihar ta yi kamarin suna. A cewar wani matashi kirkiro ma'aikatar ya canza rayuwarsa da ma ta wasu sauran matasan. Wani mai suna Danlami Tukur ya ce a jihar Gombe aka haifeshi amma galibin mutane sun sanshi da suna kalare-kalare. Ya ce shi ba dan kalare ba ne. Shi ne ainihin Kalaren. To amma yanzu Allah ya kawo lokacin da su ne suke fadakar da kawunan matasa a zauna lafiya. Ya ce gwamnan jihar ya yarda dasu ya kuma basu abin yi. Ya ce kuma an turasu Jos inda suka yi karatu. Abun da suka karanto suna anfani dashi domin inganta rayuwarsu. Yanzu kokarin da suke yi shi ne na yadda za'a zauna lafiya.
Shirin horas da matasa kan ayyukan yi da gwamnan ya kirkiro, idan ya cigaba zai taimakesu har ma da 'ya'yansu. Ya ce ba'a taba yin wani gwamna da ya zo ya nemi yadda za'a zauna lafiya kamar yadda gwamna mai ci yanzu ya yi domin an jima ana fada a jihar. Lokacin da gwamna ya yi alkawarin kawo karshen 'yan kalare wasu sun dauka wasa ne. To amma yanzu duk wanda ya ce shi dan kalare ne to ba dan garin Gombe ba ne. Zuwa ya yi. In ji Danlami Tukur babu wani sauran dan kalare a cikin garin Gombe. Sai dai wasu da suka shigo garin domin su bata harkar gwamnatin jihar. Ya ce gwamna Ibrahin Dankwambo ya ce a daina kalare, zai bada aiki kuma yana bayarwa. Ya ce gasu an basu abin yi.
Daga karshe Danlami Tukur ya roki gwamnatin Gombe ta ba wadanda ba'a basu aiki ba domin kada a jasu zuwa shiga kalare.
Ga Sa'adatu Fawu da karin bayani.