Baya ga korafe-korafe akan rasa ayyukan yi sakamakon annobar cutar coronavirus, gamayyar kungiyoyin kwadago a Najeriya sun bukaci a samar da sabbin manufofin tattalin arziki na kasa da kasa domin a samu sauyi a harkokin kwadago a nahiyar Afrika da kuma rage tasirin annobar coronavirus ga tattalin arziki da ayyukan yi.
Tun bayan bullar annobar coronavirus, masana harkar tattalin arziki suka fara nuna fargaba a kan illolin da annobar za ta yi ga tattalin arzikin kasashen duniya musamman masu tasowa kamar Najeriya.
Alkaluman kididdiga a Najeriya sun nuna cewa da yawa a cikin ‘yan kasar na rasa aikinsu saboda yadda mutane da kamfanoni ke fuskantar matsaloli ta fuskar tattalin arziki da kudaden shiga sakamakon gagarumin tasirin annobar coronavirus.
Fitaccen dan kasuwa kuma dan jarida, Mungadi Shu’aibu, ya ce idan ana so a farfado da tattalin arzikin Najeriya da ma na kasashen duniya to ya kamata a karfafa masu kananan masana’antu a kuma karfafa aikin gona saboda tasirinsa ga tattalin arzikin kasa ta hanyar samar da aikin yi ga matasa.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yamaltu Deba a jihar Gombe, Dr. Abubakar Yunusa Ahmad, ya ce annobar coronavirus ba a bangaren samar da aiki kadai ta ke barazana ba, ta shafi kowa da kowa don haka ya kamata a yi tunani mai zurfi.
Shi kuma Ministan shari’a kuma Antoni-Janar na tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, ya yi bayani akan lamarin ya ce gwamnatin tarayya ta yi kyakkyawan tanadi ta wajan bada tallafin samar da ayyukan yi.
Alkaluman kididiga a Najeriya dai sun yi nuni da cewa, tun bayan bullar annobar coronavirus kaso 40 cikin 100 na iyalan da aka yi magana da su kusan dubu biyu suka rasa ayyukan yi, lamarin da ya sa kungiyoyin kwadago suka yi ta korafi akan yadda shugabanni suka fara siyasantar da ayyukan farfado da tattalin arziki ta hanyar nuna san kai bayan fara bude zirga-zirga, ofisoshi, da masana’antu.
A kasashen duniya kuwa, annobar coronavirus ta yi sanadiyyar rasa miliyoyin guraban ayyuka kamar yadda alkaluman kididdiga na zauren tattalin arzikin duniya suka yi nuni da cewa a kasashe mafi karfin tattalin arziki na G7 kamar Amurka, an rasa ayyukan yi miliyan 30. A kasar Japan kuma mutane miliyan 1 da dubu 760 suka rasa aikin su.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf.
Facebook Forum