WASHINGTON, DC —
Sama da ‘yan gudun hijra dubu 40 masu bukatar tallafi da mafaka yanzu suke a yankin Diffa na Junhuriyar Nijer bayanda suka gudo daga jihohin arewa maso gabascin Najeriya da ke fama da tashe tashen hankula. Hukumar yan gudun hijirar Majalisar Dinkin Duniya tace shima yankin na Diffa yana bukatar a taimaka mishi don daukan dawainiyar wadanan tarin al’ummar da suka tsero don kauracewa rikicin na Boko Haram. Daga birnin Niamey ga Rahoton Abdoulaye Mamane Amadou:
Dubban mutanen Nigeria da masifar tashin hankalin ‘yan Boko Haram ta gallaba na ta kwarara zuwa cikin Junhuriyar Nijer don neman mafaka.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024