Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salman Al-Parisi Game Da Wakokin Firqatul Sahwa


دنیا کا سب سے بڑا کتب میلہ جرمنی کے شہر فرینکفرٹ میں منعقد ہوتا ہے۔
دنیا کا سب سے بڑا کتب میلہ جرمنی کے شہر فرینکفرٹ میں منعقد ہوتا ہے۔

A ci gaba da bayanin da yake yi ga filin "A Bari Ya Huce..." kan wakokin Madeeh a watan Ramadan, Salman ya tabo wakokin dake cikin faifan Ba'adal Layl

Kamar yadda aka saba cikin kowane watan Azumin Ramadan, bana ma dan jarida mai zaman kansa a kasar Sudan, Salman al-Parisi, ya shigo cikin zauren "A Bari Ya Huce" domin yi wa masu sauraron filin fashin bakin wasu wakoki.

A kashin farko na wannan fashin bakin da yayi ranar asabar 28 Yuli, 2012, watau Ramadan 9, 1433 Hijr, Salman yayi magana kan wakokin da suka hada da "Ba'adal Layl" da "Ahmad Nabiyyina" wadanda 'yan kungiyar Firqatul Sahwa Lil Intajil Fanni suka rera.

Shi dai malamin yayi zama, yana kuma da alaka sosai da garin al-Zariba ta marigayi Sheikh Abdur-Rahim Muhammad al-Bura'i, wanda ya rubuta akasarin wadannan wakoki tare da sauran shehunan malamai dake wannan gari na al-Zariba.

A saurari kashin farko na wannan hira a cikin shirin "A Bari Ya Huce..." na ranar Asabar 28 Yuli 2012.



Shirin A Bari Ya Huce

Salman A Kan Faifan Ba’adal Layl

XS
SM
MD
LG