Sallar cika ciki a Amurka na iya zama sallar da ta fi kowacce samar da nishadi, da kuma aiwatar da wasu abubuwa da mutum bai yi su ba a duk ilahirin shekarar.
Tun a shekarar 1621 kimanin shekaru 392 kenan da suka gabata, baki ‘yan share wuri zauna suka fara gabatar da wani biki na murnar kwashe albarkatun gona, da kuma nuna godiyarsu ga Allah da ba su abinci har zagayowar wata shekarar.
Bayan shekaru ana gudanar da wannan bikin don nuna godiya ga Allah da ni’imarsa, gwamnatin Amurka, a zamanin shugaba Abraham Lincoln, ta maida wannan rana ta zama ranar hutun kasa.
Wannan ranar ta sallar Cika-Ciki a nan Amurka, mutane da dama kan yi tafiye-tafiye fiye da kowane lokaci a cikin shekara.
Wannan ne kuma lokaci da Amurkawa kan hadu da dangi don zumunci da kuma cin abinci tare, kana lokaci ne da Amurkawa suka fi kauna don ire-iren abubuwa na nishadi da sukan yi a lokacin.
Kamar yadda al'adar wannan biki ta gada, shugaban Amurka kan yi afuwa ga Talo-Talo, da zimmar nuna tausayi da jin kai, ba kawai ga mutane ba har ma ga dabbobi.
Facebook Forum