A yayin da yau take jajeberin sallah karama, tuni kasuwanni a garin Kano sun cika sun tumbatsa, inda kowa ke kokarin sayan kayan masarufi domin bikin sallah.
A kan haka ne muka ji ta bakin mutane dangane da yadda zirga-zirgan jama’a a kasuwanni ke wakana ga kuma abin da suke cewa
''kayyakin sun yi tashin gwauron zabi, inda suke kokawa da rashin saukakawa da yan kasuwa ke yi a lokutan sallah karama.
Mafi yawan masu sayin na cewa duk lokacin sallah karama, lokaci ne da yan kasuwa suke tsawwalawa masu saye maimakon su yi koyi da saukakawar da suka koya a watan Ramadana.
Mun kuma zanta da masu sayar da kayyakin na dalilin da ya sa kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi, mafi yawan 'yan kasuwan na cewa a wannan lokaci, lokaci ne da kayan miya ke janyewa sannan kuma tashin farashin na danganta ne da yawan bukatar kayan miyan da ake nema sabannin yadda ake yi bukatarsu ba lokacin sallah ba.
Saurari cikakken rahoton Baraka Bashir daga Kano:
Facebook Forum