Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren tsaron Amirka ya cacaki wakilan Majalisar dokokin Amirka


Minstan tsaron Isira'ila Ehud Barak a tsakiya, shi kuma sakataren tsaron Amirka Leon Panetta daga hannu hagu a birnin Tel Aviv, kasar Isira'ila.
Minstan tsaron Isira'ila Ehud Barak a tsakiya, shi kuma sakataren tsaron Amirka Leon Panetta daga hannu hagu a birnin Tel Aviv, kasar Isira'ila.

Sakataren tsaron Amirka Leon Panetta ya la'ani wakilan Majalisar dokokin Amirka a saboda sun dakatar da taimakon raya kasa da aka yi niyar baiwa Palasdinawa

Sakataren tsaron Amirka Leon Panetta, ya caccaki wakilan Majalisar dokokin Amirka, a saboda matakin da suka dauka na dakatar da taimakon dala miliyan maitan na aiyukan raya kasa a yankunan Palasdinawa. Panetta yace wannan lokaci ne mai sarkakiya, a saboda haka bai kamata ace an dakatar da bada wannan taimako ba.

A yayinda yake magana wajen wani taron yan jarida da takwaran aikinsa na Isira'ila Ehud Barak a birnin Tel Aviv, Panetta yace wannan ba shine lokacinda ya kamata a dakatar da bada wannan taimako ba. Lokacinda jami'an Amirka suke safa da marwan kokarin shawo kan Palasdinawa da Isira'ila da su koma teburin shawarwarin samun zaman lafiya.

Ma'aikatar harkokin wajen Amirka tace, yanzu haka jami'an gwamnatin Obama suna tattaunawa gadan gadan da shugabanin Majalisar, wadanda suka ce a dakatar da bada wannan taimako.

Jami'an kungiyar raya kasashe maso tasowa ta Amirka, da ake cewa USAID a takaice, sun tabbatar da cewa dakatar da bada wannan taimako ya shafi wasu aiyuka da suke gudanarwa, to amma basu bada wani karin bayani ba.

Tunda farko a jiya litinin, Leon Panetta ya gana dabam dabam da Prime Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaron Isira'ila Ehud Barak. Haka kuma ya gana da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas da Prime Ministan Palasdinawa Salam Fayyad.

Talata aka shirya zai kai ziyara Masar. Mr Panetta yayi kira ga bangarorin biyu da su dauki matakin magance wannan matsala ta hanyar kafa kasar Palasdinu, yana mai fadin cewa babu wata zabi, fayace yin shawarwari tsakanin Isira'ila da Palasdinawa.

XS
SM
MD
LG