'Yan jihar Sokoto basu yi mamaki ba da ziyarar John Kerry zuwa daular Usmaniya a daidai wannan lokacin.
Suna cike da farin ciki da kuma fatan zata samarda wata kafa ta inganta zaman lafiya da kuma musamman kawo sauyi a yanayin da ake ciki na wuyar rayuwa saboda tabarbarewar tattalin arziki.
Wani Shehu Jatau yace ziyarar tana da matukar mahimmanci ganin irin cigaban da ita kasar Amurka ta samu a wannan karnin da ake ciki. Ziyarar zata taimaka da ganin cewa an inganta wasu abubuwa, musamman dangane da tsatsauran ra'ayi, wanda addinin musulunci bai amince dashi ba.
Shi ma Abubakar Musa yace yana ganin shawarwari ne da zasu kawo cigaba idan Allah ya yadda. Yace alheri ne.
Samaila Bundi yace zuwan John Kerry Sokoto nada mahimmanci musamman akan ilimi, wato a sa yara maza da mata makaranta a kuma nuna masu cewa a addinin musulunci da na kiristanci babu ta'adanci ciki. Ya yi la'akari da kiran da Sarkin Musulmi ya yiwa masu hannu da shuni na cewa a koyas da addinan musulunci da kiristanci a makarantu saboda mabiya addinan su taso da fahimtar juna tare.
Yanzu dai jami'an tsaro sun bazu a birnin Sokoto kama daga filin saukar jiragen sama zuwa fadar Sarkin Musulmi da ta gwamnati.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani