Abdulmalik Saidu Maibiredi, shine mai sana'ar sayar da burodi ne da aka nada a matsayin Babban Mataimaki na Musamman a shafukan sada zumunta ga Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi alƙawarin ci gaba da siyar da burodi bayan ya kammala aikinsa na ofis.
A wata wasika da ya rubuta ranar 24 ga Satumba, 2019, Malam Matawalle ya nada matashin a matsayin Mataimaki Na Musamman wanda zai fara aiki daga ranar 14 ga Satumbar, 2019.
Abdulmalik, mai shekaru 24, ya ce zai ci gaba da siyar da burodi bayan ya tashi daga aikinsa na ofis.
Da yake magana Abdulmalik ya ce “Ina matukar alfahari da sana'ata, kuma ban taba raina aikin sayar da burodin ba. Na fara sayar da burodi ne tun ina firamare."
Ya ci gaba da cewa “Na yi amfani da kudin da na samu na kasuwanci wajen biyan kudin PTA da kaina, da na jarrabawar shiga sakandare wanda ake kira common entrance a turance, da kuma jarrabawar SSCE.
“Na sayi keke ne lokacin da nake aji na 4 a makarantar firamare. Ban taɓa damuwa na tambayi iyayena kuɗi don siyan kayan sawa na makaranta ba.
“Karatun NCE di na ma, na yi shi ne ta hanyar sana’ar sayar da burodi. Yanzu haka, ina hanyar shiga shekarar karshe a Jami’ar Tarayya da ke Gusau. Wannan shine yadda rayuta ta kasance a yau. A yanzu haka ma da muke magana, burodi ne a gabana, ”in ji shi.
Facebook Forum