Shugabar rikon kwaryar Jamhuriyar Africa ta Tsakiya Catherine Samba-Panza ta bar taron shugabannin duniya na Majalisar Dinkin Duniya da ake yi anan Amurka ba shiri don komawa gida a dalilin sabon rikicin da ya barke a babban birnin kasar.
Rahotanni daga birnin Bangui na nuna cewa, an kashe mutane da dama a rikicin da ya barke tsakanin Kirista da Musulmi sakamakon mutuwar wani Musulmi. Haka ma wasu fursunoni sun tsere daga gidan yari.
Mutane 3 kuma sun mutu sakamakon taruwa a tsakiyar birnin don yin zanga-zanga zuwa fadar shugaban kasar. Masu zanga-zangar sun dora alhakin mutuwar mutanen a kan rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya da suka ce sun yi harbi cikin jama’a.
Tuni dai rundunar wanzar da zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniya ta musanta wannan zargi. Amurka ta yi tir da rikicin sannan ta yi alkawarin taimakawa kasar ta Afirka ta Tsakiya.