SHUGABANNI MAJALISAR TARAYYA: APC NA NEMAR DINKE BARAKA
Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya na cigaba da kokarin dinke barakar da ta biyo bayan zaben shugabannin Majalisar Tarayya, wadanda wasu ke ganin ba su ne jam’iyyar ke so ba. Ko bayan ziyarar da Shugaban Majalisar Dattawa Olusola Saraki ya kai wajen tsohon Shugaban Najeriya Chief Olusegun Obasanjo don nemar a rokar masa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, shi ma shugaban jam’iyyar APC Chief John Odige Oyegun ya aike da wata takardar bayani ga manema labarai, inda ya ke jaddada cewa jam’iyyar na kan kokarin ganin cewa an dinke duk wata barakar da ke akwai.
Chief Oyegun ya ce duk da yak e zaben da aka yi ya saba da abin da jam’iyyar ta so, jam’iyyar za ta yi aiki da zabin majalisar. Ya ce su na ta ganawa da ‘yan jam’iyyar da ke Majalisar don ganin yadda za a gudanar da al’amura a Majalisar ba tare da wata matsala ba. Ya sha alwashin ganin cewa APC ta dunkule wuri guda don a samu a yi wa jama’a aiki.
To saidai daya daga cikin wadanda ba su cikin zauren Majalisar yayin da aka yi zaben , tsohon gwamnan Kano Alhaji Rabi’u Musa Kwankwaso y ace bai dace a zabi ‘yan PDP cikin shugabannin Majalisar Tarayyar ba, saboda ita kanta PDP ta shafe shekaru goma sha shida, inda ta yi ta zaben shugabannin Majalisar Tarayya har sau hudu ba tare da hadawa da ‘yan wata jam’iyyar adawa ba. Ya kara da cewa hasalima bas u nan lokacin da aka zabi shugabannin, don haka ba za su amince ba.
To saidai dan Majalisar Dattawa Ali Ndume, wanda aka kayar a zaben Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma dan bangaren da ake kira “Like Minds” y ace tafiya da ‘yan PDP ya zama dole muddun ana so a yi dokokin da su ka shafi kundin tsarin mulkin kasa. Y ace ‘yan APC kadai ba za su iya samar da 2/3 na ‘yan Majalisar da ake bukata a dokance ba.