Rundunar 'yan sandan jihar Abia ta ce ta cafke wasu fiye da tamanin wadanda ake zarginsu da yin garkuwa da mutane yayin da ita kuma gwamnatin tarayyar Najeriya ke kokarin shawo kan ta'addanci a duk fadin kasar..
Kwamishanan 'yan sandan jihar Mr. Anthony Ogbuizi shi ya bayyana wa Muryar Amurka hakan jiya Lahadi inda ya kara da cewa galibin mutanen yanzu suna zaman jiran shari'a.
Dangane da abun da rundunar 'yan sandan ke yi domin kawar da kungiyar 'yan bata gari, musamman a daidai wannan lokacin da jama'a ke shirin bikin Kirsimati, tare da dakile shigo da miyagun makamai, sai kwamishanan ya ce akwai motoci na musamman da suka umurci jami'ansu su tabbatar an tantancesu. Baicin motocin, inji kwamishanan akwai irin mutanen da dole sai an tantancesu.
A cewar kwamishanan shigo da makamai cikin jihar ta wata barauniyar hanya zai yi matukar wuya. Akwai kuma wasu matakai masu tasiri da 'yan sanda zasu daukai da kwamishanan ya ce ba zasu bayyana ba domin tabbatar cewa an kakkabe ayyukan asha daga jihar gaba daya.
Ga rahoton Alphonsos Okoroigwe
Facebook Forum