Rundunar hadin gwiwa ta kasashen tafkin Chadi ta yi ikirarin cewa tana dap da murkushe sauran ‘yan Boko Haram dake yankin.
Kakakin rundunar Kanar Mustapha Anka yace a gefensu hadin kan ya taimaka kwarai wajen shawo karfin Boko Haram. Yace basu kadai suke aikin ba saboda suna samun labaran sirri daga kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da wasu kungiyoyi.
Baicin taimakaon da suke samu, rundunar sojojin Najeriya na shirya taruka na kasa da kasa akan harkokin tsaro da yadda ake yakin sunkuru. Kasashe irin su Amurka, Masar, Nijar da sauransu suna halarta.
Kanar Umar Ali wanda ya fito daga Nijar ya ce ya zo Najeriya ne domin halartar bita ta kasa da kasa akan tsaro. A cewarsa, tun da suka dauki matakai da dama matsalar ‘yan ta’ada ta ragu a kasar ta Nijar.
To saidai a makon jiya wasu ‘yan ta’adda sun halaka wasu sojojin Jumhuriyar Nijar a kan iyaka da kasar Mali, abin da ya sa masana harkokin tsaro irinsu Major General Yakubu Usman mai ritaya ke ganin ya kamata a janyo kasar Mali cikin rundunar hadin gwuiwar kasashen tafkin Chadi. Yace, ‘yan ta’addan da suka kai hari Nijar daga Libya suka fito.
Hassan Maina Kaina na da karin bayani.
Facebook Forum