Rundunar mayakan saman Najeriya ta fara jigilar kayayyakin tallafin rage radadin annobar Coronavirus da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma tare da hadin gwiwar kasashen Turai da kuma hukumar raya kasashe ta MDD suka bayar da taimako.
Da take kaddamar da fara aikin jigilar tallafin a babban filin jiragen saman a kasa da kasa dake Abuja, jagorar tawagar kuma mataimakiyar shugabar hukumar ECOWAS, Finda Koroma, ta ce akwai butakar samar da isassun kayayyakin aiki kiwon lafiya da magunguna don shawo kan sake bullar cutar a karo na biyu.
Linda ta ce tun a watan Agustan bara rundunar sojin saman Najeriya ta fara taka rawa wajen aikin jigilar kayayyakin tallafi na magunguna zuwa kasashen yammacin Afirka.
Tun bullar cutar coronavirus sojojin saman Najeriya sun yi jigilar kayan tallafin magunguna da hamshakin attajirin kasar China, Jack Ma, ya bayar da tallafinsu.