Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar JTF Ta Kama Shugaban ANPP Na Jihar Borno


Wasu daga cikin sojojin da gwamnatin Najeriya ta girka a yankin arewa maso gabashin kasar domin yakar 'yan Boko Haram
Wasu daga cikin sojojin da gwamnatin Najeriya ta girka a yankin arewa maso gabashin kasar domin yakar 'yan Boko Haram

Haka kuma rundunar ta killace wata unguwa mai suna Bulabulin Nganeram a cikin Maiduguri inda aka yi imani 'yan Boko Haram sun mamaye ta bayan sun kori mazauna unguwar daga gidajensu.

Rundunar tsaron hadin guiwa, wadda aka fi sani da sunan JTF, a Maiduguri, ta tabbatar da labarin cewa lallai tana tsare da shugaban jam'iyyar ANPP na Jihar Borno, Alhaji Mala Othman, dangane da binciken wasu batutuwan da suka shafi sha'anin tsaron kasa.

Da yake tabbatar da haka ga wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Maiduguri, kakakin rundunar ta JTF, Leftana-Kanar Sagir Musa, yace an damke shugaban na jam'iyyar ANPP kwanaki hudu zuwa biyar da suka shige.

A bisa dukkan alamu, an kama shi ne jim kadan a bayan da matasa 'yan banga dake farautar 'yan Boko Haram a Maiduguri, suka kai farmaki a kan gidan jami'in suka banka masa wuta.

Kanar Sagir, ya kuma gaskata labarin cewa dakaru sun killace Unguwar Bulabulin Nganeram a Cikin Maiduguri, inda ake gudanar da abinda ya kira "yaki da ta'addancin da ya mamaye wannan unguwa."

Yace sun samu makamai da yawa, sun kuma kashe ko sun kama 'yan Boko Haram masu yawa cikin wannan unguwa.

Kwanakin baya aka yi ta jin labarin cewa 'ya'yan Boko Haram sun sulale suka mamaye wannan unguwa, a bayan da ko dai suka kori mazauna unguwar karfi da yaji, ko kuma su mazauna unguwar suka gudu daga gidajensu da kawunansu a bayan da 'yan bindigar suka fara shiga su na zama cikin wannan unguwa.

Sojojin su na bi gida-gida cikin wannan unguwa, su na farautar makamai da 'yan bindigar da suka boye su. An ce har yanzu ana gwabzawa a tsakanin su jami'an tsaro na rundunar JTF da wadannan 'yan bindiga dake kokarin sajewa da jama'a.

Haka kuma, sojojin sun ce sun gano, kuma su na kira ga jama'a da su yi hattara sosai da 'yan bindigar da suke shiga su yi lullubi kamar mata domin su sulale ko kuma su je aikata wani mummunan aikin a wani wuri.

Ga cikakken bayani a tattaunawar Haruna Dauda da Kanar Sagir Musa:

Rundunar JTF Ta Kama Shugaban Jam'iyyar ANPP Na Jihar Borno - 3:31
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG