Tun dai lokacinda aka tura jami’an tsaro na hadin gwiwa da ake cewa JTF a takaice zuwa Maiduguri, mazauna garin da wasu suke kira ga gwamnatin Nigeria cewa ta janye sojojin, domin suna cin zafarin mutane. Ana cikin haka ne kuma asabar din nan wakilin sashen Hausa Haruna Dauda Biu ya aiko mana da rahoto cewa mazauna unguwar Budum a Maiduguri sunyi zargin cewa daya daga ciki jami’an tsaron rundunar JTF, wani dan sanda ya harbe wata yarinya yar shekara goma sha uku har lahira.
A lokacinda wakilin sashen Hausa yaje unguwar, ya iske daruruwan mutane da suka taru suna nuna fushinsu da rashin amincewarsu. Ya kuma ga gawar yarinyar da aka rufe da ganye. Wasu mazauna unguwar sun fada wa wakilin sashen Hausa cewa sun ga lokacinda da dan sandan ya harbe yarinyar.
Abubakar Tijjani, dan Majalisar dake wakiltan birnin Maiduguri da kewaya shima yana wurin, harma ya yi barazanar a cewa,idan har gwamnati ba zata janye sojojin ba, to zaiyi murabus, domin ba zasu zura ido suna ganin yadda jami'an tsaro ke tozarta mutane ba.
Daya daga cikin manyan jami'an rundunar ta hadin guiwa JTF, Kanal Victor ya shedawa wakilin sashen Hausa, shi babu abinda zai ce a yanzu, amma dan sandan da yayi harbin yana hannu.