Shahararen dan wasan kwallon kafa na duniya dan kasar Putugal, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Juventus Cristiano Ronaldo, ya kafa tarihin sayen mota mafi tsada a duniya.
Dan wasan wanda ya taimaka wa kulob dinsa Juventus, ta lashe gasar Seria A na Itali a karo na takwas a jere, bana Ronaldo ya sayi motar kirar kamfanin Bugatti, mai suna “La Voiture Noire” da faransanci, a Hausance kuma a na nufin 'Bakar Mota' kan zunzurutun kudi har Euro miliyan €11, wato kwatankwacin naira Biliyan 4 da miliyan 448, da dubu 883, da dari 862.
Wannan mota “La Voiture Noire” dai irinta guda daya kacal kamfanin motocin na Bugatti ya kera a halin yanzu, a wani bangare na bikin murnan cikarsa shekaru 110 da fara kere-kere a duniya tun daga 1909 zuwa 2019 kenan.
Sai dai dan wasan Cristiano ba zai hau motar ba har sai shekara ta 2021, saboda akwai sauran nazarin da kamfanin na Bugatti ke karasawa akanta.
Dan wasan yana daukar fam dubu dari biyar £500 duk sati a matsayin albashi a kungiyar kwallon kafa ta Juventus dake kasar Itali.
Facebook Forum