A wani babban taron da ta yi a Abuja tun bayan munanan rikice-rikicen da aka yi tsakanin manoma da makiyaya a jahohin Benue da Taraba da Adamawa, kungiyar Miyatti Allah ta Fulani ta yi kiran da a hukunta duk wani mai laifi muddun an tabbatar da laifinsa. Kungiyar ta ce ta na mai yin Allah wadai da duk wani salon tashin hankali da masu yin tashin hankalin.
Kungiyar ta jaddada cewa babu ruwanta da tashin hankali kuma abin da ta sa gaba shi ne kare muradun makiyaya kamar yadda doka ta gindaya. Ta ce ta damu da yadda akan alakanta Fulani da tashin hankali ko mallakar makamai da kuma yadda wasu ke cewa a ayyana kungiyar Miyatti Allah a matsayin ta ‘yan ta’adda.
Meyatti Allah ta ce sam ba ta duk wani ra’ayi na tashin hankali. Hasali ma, shugaban kungiyar a matakin kasa, Ardon Zuru Muhammadu Kirwa ya ce sam kar a ragar ma duk wanda aka tabbatar da laifinsa. Ya ce duk wadanda aka kama da bindiga a ayyana su da matsayin ‘yan ta’adda. Ardo ya kara da cewa Miyatti Allah ba kungiya ba ce ta boye masu laifi. “Ko ni ne aka sami Ina da hannu cikin ta’addanci na goyi bayan hukuma ta gayyace ni ta kama ni ta hukunta ni; balle wani wanda ke baya na, wanda na ke shugabantar shi.”
Ga dai wakilinmu Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:
Facebook Forum