Jam'iyyar APC a jihar Gombe ta shiga wani rudani inda tace ta dakatar da mataimakin shugaban jam'iyyar na jiha Mr. Simon Dauda Tula a wata takarda da shugaban jam'iyyar Barrister Magaji Duhu ya sanyawa hannu.
Bayanin dake kunshe cikin takardar ya nuna cewa an dakatar da mataimakin shugaban ne sabili da yiwa jam'iyyar zagon kasa.
Yayin da wakiliyar Muryar Amurka ta tunkari shi Mr. Simon Dauda Tula yace shi bai san ma'anar an dakatar dashi ba domin ya riga ya sanar da jam'iyyar cewa ya ajiye mukaminsa kuma ya fice ya koma PDP. Ya tura wasikar ne tun ranar 26 ga watan Yuli inda ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar. Amma kwana biyu bayan ya bayar da tashi wasikar sai suka kawo masa wata suna shaida masa cewa an dakatar da shi na wucingadi domin ana zarginsa da yiwa jam'iyyar zagon kasa. Ba'a taba bincikarsa ba ko a rubuta masa takardar zarginsa da wani laifi ba.
A wasikar da ya rubuta yace ya fice daga jam'iyyar tun daga ranar farko ta watan Agusta lamarin da yace tamkar ya mutuntasu ne domin bai fito fili ya fadawa duniya ba. Yace abun da suka yi ya bashi dariya.
Dangane da dalilin barin jam'iyyar APC Mr Simon Dauda yace mutum baya siyasa domin kashin kansa sai domin mutane. Mutanensa sun matsa ya koma PDP domin gwamnatin PDP tana yiwa mutanensa ayyukan cigaba. Yace ya gamsu da dalilan da suka bayar.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.