Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigimar Jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Wani jigo cikin gungun wasu jiga-jigan 'yan PDP da su ka fishe daga jam'iyyarsu su ke kuma tunanin mataki na gaba, gwamnan jihar Kano Alhaji Rabiu Musa, ya ce su matakin da jama'a ke so za su dauka.

Wani jigon sabuwar jam’iyyar PDP da hukumar zaben Nijeriya da kotu su ka haramta, Gwamnan Kano Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso ya ce rashin kyautatawa ne ya kawo tsaguwa cikin jam’iyyar ta PDP mai mulkin Nijeriya. Ya ce sun yi ta kiraye kirayen a gyara abubuwa amma aka yi biris. Y ace wasu abubuwan ma saboda tsananin muninsu bas u iya fada a bainar jamma’a saidai kawai ga shugabanni.

Gwamna Kwankwaso ya gaya ma wakilinmu da ke Fadar Shugaban Nijeriya a Abuja Umar Faruk Musa

cewa su tara su ka zabi Rotimi Amaechi a matsayin shugaba amma aka yi kokarin dannewa a bai wa wanda ya ci kuri’u 16. Ya ce kuma a jihar Rivers an cire masu shugabanni ba bisa ka’ida ba, sannan sun ce a je a gyara al’amura amma an kasa.

Ya ce ko ga batun sauran abubuwan da su ka shafi tsarin shugabanci da yaki da rashawa. Wannan ma in ji shi an kasa gyarawa. Y ace su a Kano sun a shugabanci ne ta wajen nuna misali. Shi ya sa, in ji shi, a Kano ba wanda zai yi sata hankalinsa kwance.

Dangane da fitar su jam’iyyar PDP karkashin shugabancin Bamanga Tukur kuwa, Gwamna Kwankwaso ya ce makomarsu ta dogara ne kan yadda jama’a su ka so. Y ace a yayin da wasu ke son a kafa sabuwar jam’iyya; wasu kuma so su ke a shiga jam’iyyar APC. Ya ce daga karshe su dai abin da jama’a ke so za su yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG