Madugun ‘yan adawar kasar Sudan ta Kudu Riek Machar, ya koma kasarsa yau Asabar.
Ana sa ran zai gana da shugaba Salva Kiir a kokarin da kasar ke yi na kafa gwamnatin hadin gwiwa.
Duka shugabannin biyu su na da kasa da wata daya su cimma matsaya, bisa ga wata yarjejeniya da suka rattabawa hannu shekara daya da ta gabata.
A shekarar 2011 Sudan ta kudu ta sami ‘yancin kai daga makwabciyarta Sudan, amma a karshen shekarar 2013 tashin hankali ya barke a kasar akan gwagwarmayar rike madafun iko tsakanin shugaba Kiir da Machar, mataimakin shugaban kasa. Fadan da aka yi a kasar yayi sanadiyar mutuwar dubban ‘yan Sudan ta Kudu ya kuma tilastawa miliyoyin ‘yan kasar tserewa daga gidajensu.
Machar na neman tabbacin kare lafiyarsa kafin ya koma Sudan ta kudu zaman din-din-din.
Cikin mataimakan shugaban kasa guda biyar, Machar ne za a nada na daya a karkashin gwamnatin hadin gwiwar.
Facebook Forum