Lemo ya kunshi abubuwa da yawa – kamarsu Citric acid, calcium, magnesium, Vitamin C, bioflavonoids, pectin da limonene – wadanda suke kawo kariyar jiki da yaki da cututtuka.
Yadda za’a hada shi:
Yi amfani da ruwa mai tsabta, mai dumi. Banda ruwan sanyi. Kowanne lokaci kayi amfani da sabon lemo, ba wanda akasa a kwalba ba. Ka matse shi cikin rabin kofi, sai ka sha na farko da safe kamin ka ci wani abinci ko kuma kamin kayi wani aiki da sauransu.
Ribarsa / Sakamako
• Taimako: Ruwan lemo yana kauda abubuwa marasa kyau da illa daga jiki. Abinda ya kunsa yayi kamada miyau da hydraulic acid na ruwan narke abinci. Yana taimakon hanta fitar da matsarmama, wadda take da guba da kuma ake bukata wajen narkewar abinci. Lemo yana taimakawa jiki da Vitamin, kuma yana taimako wajen rage dafi daga hanyar narke abinci.
• Tsabtace Ciki: Ruwan lemo yana fitar da abubuwa marasa kyau da ba’a so daga cikin jiki, domin yana kara yawan fitsari. Don haka abubuwan dafi suna fita da sauri. Citric acid cikin lemo yana rage aiyyukan enzyme, wanda ke sa matsarmama ta rage dafi.
• Kara karfin kayan yakin jikin mutum (immunity): Lemo yana da yawan sinadarin Vitamin C, wanda yake da karfin yaki da sanyi. Yana taimakon kwakwalwa yin aiki domin yana da sanadarin da ake kira potassium, wanda yake rage karfin zubar jini, yana kuma kara shigar iron cikin jiki wanda ke taimako wajen aikin kariyar jiki. Cikin lemo akwai wani abu wanda ke taimakon kiyaye sanyi da sauransu.
• Daidaita kimanin PH: Lemo na cikin kayan abinci masu bauri cikin jiki. Su kansu masu tsami ne, amma cikin jikin mu, suna zama da bauri ne. Yawancin rashin lafiya na aukuwa domin rashin daidaituwar PH. Shan ruwan lemo koyaushe yana rage wannan tsami daga jikinmu. Wanda shine ke kawo zafi da ciwo gare mu.
• Yana gyara fatar jiki: kayayyakin Vitamin C da sauran abubuwa masu yaki da dafi suna kauda ciwuka daga fatar jikin mu. Lemo yana maganin zafi da ciwo daga ciki zuwa wajen fatar jiki, saboda yanayin tsami da bauri na shi.
• Kara karfi da yanayin mutum: muna samun kari daga abincin da muke ci, yayinda ya narke ya bada abinda ake bukata. Kanshin lemo yana taimakon yanayin mutane da Karin karfi. Bincike ya kuma nuna cewa kanshin lemo yana kwantar da zuciyar mutum ya kuma rage damuwa da bacin rai.
• Inganta warkewa:Vitamin C da yake da yawa cikin lemo, yana inganta warkewar ciwuka, kuma yana inganta lafiyar kasusuwa da sauransu. Yana taimako kwarai wajen inganta lafiya mai kyau.
• Sabunta numfashi: Lemo yana sabunta numfashi da rage zafin ciwon hakori. Kayi hankali da citric acid zai iya zarge tushen hakori. Kada ka goge baki nan da nan bayan shan ruwan lemo, yafi kyau ka goge baki kamin ka sha. Kuma zaiyi kyau ka kuskure baki da ruwa bayan ka sha.
• Maida Ruwa cikin jiki: Ruwan dumi da ruwan lemo suna taimakon kayan yakin jiki ta wurin mayar da ruwa cikin jiki. Yayinda jikin ka ya rasa ruwa sosai, zaka ji illarsa kamarsu: gajiya, rashin karfi, rashin karfin kayan yakin jiki, rashin kuzari, rashi / yawan karfin jini, rashin barci, rashin tunani mai kyau da sauransu.
• Yana rage girman jiki ko kiba: Lemo yana da yawan Pectin fibre, wanda yake yakin abubuwan da ke kawo yunwa. Bincike ya nuna mutane masu yawancin bauri a abincinsu, sune rage kiba da sauri.