Mubarak Shuaibu Sulaiman, matashi da yake gudanar da karatun shi a matakin digiri na biyu a jami'ar Coventry dake kasar Burtaniya. Yana zurfafa karutu inda yake bincike a fanin da ya shafi hako albarkatun mai da tsaftar muhalli a kimiyance 'Petrolium and Enviromental Technology' a turance.
Yayi muna gamsassun bayanai dangane da yadda karatun shi ke gudana a jami'ar, kana da wasu hanyoyi da yake ganin cewar matasa a Najeriya ya kamata subi don cin gajiyar kuruciyar su.
Don jin cikakkiyar hirar mu sai kun latsa shirin a kasa.
-
Yusuf Harande
Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.