Hukumomi a Najeriya sun ce zasu bude tashoshin jiragen sama don zirga-zirgar fita da kuma shigowa kasar, daga ranar Asabar mai zuwa, a karon farko bayan watanni biyar da rufewa.
Tun a ranar 23 ga wata Maris gwamnatin kasar ta dakatar da shige da ficen jirage, a dalilin dakile yaduwar annobar coronavirus.
Gwamnatin ta ce jirage hudu na farko da zasu shigo daga kasashen ketare zasu fara sauka ne a birnin tarayya Abuja. Sai birnin Lagos, amma ya zuwa yanzu ba a bayyana ko daga ina wadannan jiragen zasu zo ba.
A cewar ministan sufurin jirage Hadi Sirika, matakin bude wannan shine, ganin yadda ba a samu wata matsalaba tun bayan bude hada-hadar jiragen na cikin gida a ranar 8 ga watan Yuli.
Sirika, ya kara da cewar za a tabbatar da cewar an bi duk ka’idodji da suka kamata wajen ganin an samu nasarar dawowar zirgar-zirgar jirage.
Facebook Forum