Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar 15 ga Watan Janairun Kowace Shekara Ranar Tunawa ce da Mazan Jiya a Najeriya


Dakarun Sojojin Najeriya
Dakarun Sojojin Najeriya

Najeriya ta kebe ranar 15 ga kowane watan Janairu a matsayin ranar tunawa da sojojin da suka sadakar da rayukansu domin kasar.

Najeriya ta kebe ranar 15 ga watan Janairun kowace shekara a ranar tunawa da askarawan kasar da suka kwanta dama yayin yakin basasar kasar da kuma wadanda har yanzu suna da rai.

An ware ranar ne domin tunawa da 'yan mazan jiya da suka fafata domin su tabbatar da kasar ta dunkule ta zama kasa daya. A wannan ranar a kan yi addu'o'i tare da faretin bangirma domin karamawa.

Game da ranar wasu cikin mazan jiyan sun ce abun kunya ne kuma abun tausayi ne. Ali Kachalla wanda ya yi aiki da sojojin Najeriya har tsawon shekaru 32 ya ce abun banhaushi ne idan a ka yi la'akari da yadda gwamnatin tarayya take wulakanta sojojin da suka ajiye rigunansu. Ya ce wadanda suka yi yaki kana suka bar aiki duk alkawuran da aka yi masu babu wanda aka jika. Ya ce lamarin abun kunya ne. Ya ce bai kamata sai sun yi kuka a jisu ba.

Shi ma wani tsohon sojoja kuma sakataren tsoffin sojojin Najeriya reshen jihar Adamawa Nelson Tagashi ya bayyana halin da suke ciki. Ya ce wasu sun yi ritaya ba'a biyasu ba. Wasu sun bar aiki ko domin karaya lokacin aiki ko makanta amma an barsu ba'a biyasu ba. Ya ce suna fuskantar biyan kudin makarantun yara da kuma shiga kasuwa sayen abinci. Duk wadannan abubuwa sun kawo masu damuwa. Idan akwai rashin lafiya dole ne a nemi kudin magani amma kuma ga rashi. Ya ce alkawarin da gwamnati ta yi masu na biyan a kalla kashi 50 na hakinsu sun biya kashi 30 ne kawai sauran sun yi shiru.

Sanin kowa ne cewa a duk shekara a na yin wannan bikin tunawa da 'yan mazan jiya domin a jinjinawa irin rawar da suka taka wajen tsare rayuka da ma dukiyoyin al'umma da kuma hubbasan da suka yi na tabbatar da kasar ta kasance kasa daya al'umma daya.Dalilin haka ne majalisar dattawan kasar ta jaddada mahimmancin ranar. Majalisar ta ce ya kamata a tallafawa 'yan mazan jiyan domin inganta tsaro.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG