Yayin da aka shiga watan azumi na Ramadana, shugaba Buhari na Najeriya ya baiwa 'yan Najeriya shawarwari kan yadda ya kamata su gudanar da al'ammuransu cikin wannan yanayi da ake ci gaba da fama da Coronavirus.
A cikin wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, Shugaban ya yi wa musulmai a duk fadin duniya fatan Alheri yayin da aka fara azumi.
Shugaban ya jadadda muhimmancin mayar da hankali kan 'yan uwantaka da kuma taimakawa mutanen da ke da bukata.
A cewar shugaban, watan Ramadana ta shekarar nan ta zo a lokaci mai cike da rashin tabbas yayin da duniya gabaya ke fama da annobar Coronavirus.
Ya ce "wannan annobar da ta yadu a fiye da kasashe 200, ya janyo bukatar kaucewa tarurrukan mutane da yawa"
Shugaban ya shawarci 'yan kasar da su kaucewa haduwa da mutane domin shan ruwa tare ko kuma gudanar da sallar jam'i da mutane da yawa.
A karshe shugaban ya kara da cewa, "amma fa rashin iya gudanar da abubuwa yadda aka saba cikin Ramadan, bai kamata ya zamo wa mutane dalilin kin yin azumi ba."
A kasar ta Najeriya, mutum kusan 1000 ne ke fama da cutar Coronavirus wacce za ta hana a gudanar da ibada yadda aka saba cikin wannan watan na Ramadana.
Facebook Forum