Injiniya Ahmed Zakari Ngoroje mai kula da harkokin Shugaba Buhari a jihar Taraba y ace matakin da majalisar ta dauka abun mamaki ne. Amma a wani bangaren bai bada mamaki ba saboda shugaban kasa ya lashi takobin cewa duk wanda ya saci kudin Najeriya dole ne a kama shi, ya kuma dawo da kudin.
A cewarsa mutanen dake neman tsige shugaba kasa ba zasu ci nasara ba saboda kawunan ‘yan Najeriya sun waye. Ya yi musu gargadi da su yi hankali da kokarin tsige shugaban kasa su yi hankali saboda talakawan kasar sun kai bango. Suna hakuri ne kawai saboda yadda shugaban kasa ke tafiyar da ayyukansa.
Sani Tahir, wani dan jarida dake zaune a Abuja cewa ya yi su ‘yan majalisa akwai kundun tsarin mulki da ya basu dama kuma akansa suka boyewa, saboda haka duk abun da suka ce zasu aiwatar idan ba’a natsu ba an zauna an tattauna domin a kai zuciya nesa za’a yi “da na sani” za’a kuma ji kunya domin abun da ake tsammani ba zasu yi ba suna iya yinsa. Yace su ne suke da doka a hannunsu.
Tsohon Dan Majalisar Wakilai Barrister Ibrahim Bello shi ko cewa ya yi ‘yan Najeriya sun sha wahala tun daga shekarar 1999 kuma an yi barna amma gyara na da wuya. ‘Yan Najeriya na kabilu daban daban da Kiristoci da Musulmi sun yadda da Shugaba Buhari. A cewarsa wasu gwamnoni da wasu ministoci da wasu ‘yan majalisa su ne basa son shugaba Buhari, su ne suke neman tada hankali. Suna son su cuci Najeriya ne. Yayin da shugaban ke kokarin yin gyara.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Facebook Forum