Muryar Amurka ta bi jama'a domin jin ra'ayoyinsu akan kamawa da tsare tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da 'yansanda suka yi.
Umar Bello a nashi ra'ayin yana ganin babu abun da ya cancanta ga dan Adam baicin zaman lafiya. Yace idan gaskiya ne yana kalamun tunzura mutane yakamata ya hakura ya nemi zaman lafiya. Ya kira bangaren gwamnatin Jigawa da shi Sule Lamido su nemi zaman lafiya.
Shi kuwa Ahmed Ali cewa yayi matsala ce tsakanin gwamnan jihar Badaru da shi Sule Lamido amma abun da zai kawowa jihar cigaba ake bukata. Ya kamata shugabanni suna daidaita kansu yadda talakawan zasu ga abun da ake yi masu.
Wani kuma yana ganin siyasa ce kawai. Bai kamata a ce jami'an tsaro sun dauki wani bangare ba domin su ba 'yan siyasa ba ne. Yace domin wani yayi taron siyasa bai kamata a ce an daureshi ba domin kowa yana da 'yancin yayi siyasarsa
A cewar wani lamarin wani kalubale ne ga jami'an tsaro. Yace idan akwai zargi ko korafi akan mutum ya kamata su yi kyakyawan duba kada a shigo da siyasa a ciki. Doka ta ba kowa izinin yayi taro muddin ya bi hanyar da ta kamata. Kana yace a auna kalaman da yayi , shin sun kai kalaman da zasu sa a tsareshi. Ya kira a yiwa Sule Lamido adalci.
Wani yace a kasar akwai wasu gwamnoni da suke kalamun harzuka mutane amma ba'a kamasu ba. Saboda haka ya kamata jami'an tsaro su san aikinsu ba na 'yan siyasa ba ne. Shi ma Sule Lamidon ya kamata ya daina wasu kalaman da zasu kawo tashin hankali domin duk inda babu kwanciyar hankali ba za'a samu cigaba ba.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Facebook Forum