Taron na hadin gwuiwa tsakanin kasashen turai da wasu kasashen Afirka, musamman wadanda matsalar bakin haure da ta 'yan gudun hijira ta fi shafuwa kamar kasashen Nijar, Chadi da Libiya da kasar Faransa ta jagoranta ya maida hankali ne akan yadda kasashen zasu hada karfi da karfe wajen yakar matasalar bakon hauren.
Akwai yadda matasan Nijar suka kalli taron. Tabila Rabiu daya daga cikin matasan Nijar yana mai cewa idan shugabanninsu sun zama 'yan kallo a taron kasashen, turawa zasu cusa masu nasu bukatun ne shugabannin Afirka su aiwatar a cikin kasashen Afirka. Idan hakan ya faru a cewar Rabiu "asha" Idan an ce ga ciwo dole ne su san maganinshi ba matsayin turai ba.
Saidai a taron kasashen turai su ce zasu cigaba da taimakawa kasashen Afirka da suka halarci taron domin magance matsalar ta bakin haure.
Sidi Muhammad na majalisar matasan Nijar ya ga ya kamata a kafa wani tsari na musamman da zai kula da taimakawa matasan kasar. Yana mai cewa idan aka samu kudin taimakawa kasashen kamata ya yi a yi anfani da kudaden da shirye shiryen da zasu anfani matasa. Dole ne gwamnati ta yi nazarin abubuwan da zasu taimakawa matasa kamar bunkasa ma'aikatau walau na hannu ko kamfanonin sadarwa. A samar da shirin da zai horas da matasa ayyukan hannu ba karatun boko ba zalla.
Amma duk wani tsari da za'a bullo dashi na taimakawa matasa ba zai yi wani tasiri ba idan ba'a dama dasu ba. Suna mai cewa idan shugabansu ya dawo daga taron ya kamata ya zauna da matasa ya bayyana masu abubuwan da za'a yi masu.
Kawo yanzu kimanin mutane 140,000 ne suka rasa rayukansu a kokarinsu na ketarewa zuwa turai ta hanyar da bata dace ba tun daga shekarar 2014.
Ga rahoton Yusuf Abdullahi da karin bayani.
Facebook Forum