Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

QATAR 2022: Amurka Ta Kimtsa Ko Ta Doke Iran Ko Kuma Ta Tattara Ta Koma Gida


Gregg Berhalter
Gregg Berhalter

Kimanin shekaru 24 kenan da Amurka ta fafata da kasar Iran. A waccan lokacin Amurka bata ji da dadi ba a wasan da ta yi da Iran a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a kasar Faransa a shekarar 1998, inda Iran ta doke Amurka da ci 2-1, lamarin da ya yi sanadiyar ficewar Amurka daga gasar.

Idan kocin Amurka, Gregg Berhalter ya kudiri aniyar shiga kunya ta biyu ta ficewa tun daga matakin farko akwai bukatar ya bada kykkyawan jagoranci ga tawagarsa a ranar Talata a fafatawar da kasashen biyu masu adawa da juna a siyasance zasu yi a filin wasa na Al Thumama.

Za a yi tambaya da sosaigame da mai horar da Amurka Berhalter da takwaransa na Iran, Carlos Queiroz, toh sai dai, wannan wasan ba zai zo ne kawai daga dabaru ko yanke shawarar masu horaswa ba.

Yan wasan Kwallon Amurka
Yan wasan Kwallon Amurka

Adawar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi kamari tun cikin watan Afrilu da aka karkasa kasashen da zasu fafata da juna a cikin rukunoni a gasar, kuma abubuwan da suka faru a gasar ta Qatar ba su yi wani tasiri ba wajen kawar da wannan kiyayyar.

Kasashen da ke cikin rukunin B sun hada ne da Ingila, Iran Amurka da kuma Wales. Ingila tana da maki 4 da kwallaye 4, itama Iran tana da maki 3 da kuma bashin kwallaye 2. Amurka da bata yi kuma ba a yi nasara a kanta ba tana da maki 2 amma babu kwallo, sa’annan Wales tana da maki 1 da bashin kwallaye 2. Kasashe biyu da zasu yi fice sune zasu wuce matsayi na biyu na ‘yan 16.

A duk tsawon wannan gasar cin kofin duniya, ana tambayar tawagar Iran game da zanga-zangar da aka yi a kasarsu, watanni biyu da aka shafe ana tashe tashen hankula bayan mutuwar wata mata 'yar shekaru 22 a hannun jami'an 'yan sandan da’a a kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar masu zanga-zangar 410.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG