Bayan kwashe tsawon lokaci suna karawa da kungiyoyi da dama, ‘yan wasan Kano Pillars a karon farko, sun samu nasara a wannan kakar was ta bana.
A jiya ne dai kungiyar ta yi nasarar zura kwallo a ragar kungiyar Akwa Starlets da ci 2-1, a wasan da aka buga a filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo.
Gabanin wannan karawa, Pillars ta yi kunnen doki da kungiyar Rivers United a wasan farko, kana Lobi Stars ta lallasa ta da ci 0-1.
Sai kuma karawarsu da Wikki Tourist inda ta lallasa su da ci daya mai ban haushi.
Kana a mako na 6, ta kara tsakaninta da Plateau United da Jigawa Goldens in da su ma suka yi kunnen doki 0-0.
Da ma Kano Pillars ce kungiyar da ba ta samu kwallo ko daya ba, a cikin jerin kungiyoyin da ke buga wasan na gasar cikin gida, cikin wasannin 5 da suka buga.
Amma wasu na ganin dawowar tsohon kocinsu Rabiu Ali, ya sa kungiyar ta farfado.
Facebook Forum