Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Peter Obi, Dino Melaye, Sun Jajantawa Ekweremadu Bisa Halin Da Ya Shiga


Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi (Hoto: Twitter/Peter Obi)
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi (Hoto: Twitter/Peter Obi)

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Obi ya ce sun dukufa wajen yi wa Ekweremadu da mai dakinsa addu’a wajen ganin ‘yarsu ta samu lafiya.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Labor Party (LP) Peter Obi, ya jajantawa tsohon mataimakin kakakin majalisar dattawan Najeriya Ike Ekweremadu bisa halin da ya tsinci kansa a ciki.

Rahotanni sun yi nuni da cewa hukumomi a birnin London suna tsare da Ekweremadu da mai dakinsa Beatrice bisa zargin yunkurin cire wani sashi na jikin dan adam.

A ranar Alhamis aka gurfanar da su a wata kotun Majistret, an kuma ki ba da belinsu kana kotun ta dage karar zuwa 7 ga watan Yuli.

Rahotannin da jami’an tsaron birnin na London suka fitar sun nuna cewa, an kama Ekweremadu da matarsa bisa zargin suna yunkurin cire wa wani yaro wani sashi na jikinsa.

Bayanai sun yi nuni da cewa Ekweremadu yana da wata ‘ya mai larura da ke bukatar koda, kuma ana zargin ta yaron za a cire saka mata.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Obi ya ce sun dukufa wajen yi wa Ekweremadu da mai dakinsa addu’a wajen ganin ‘yarsu ta samu lafiya.

“Ni da iyalina, muna tare da Ekweremadu kan halin kakanikayi da ya shiga. Za mu dukufa wajen yin addu’a domin fatan Allah ya ba ‘yar su lafiya ya kuma tabbatar da adalci.” In ji Obi.

A daya gefen kuma, tsohon Sanata, Dilo Malaye, wanda ya wakilci Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawan, ya fito ya nuna goyon bayansa ga Ekweremadu, inda ya wallafa wata wasika da ke nuna cewa, Ekweremadu ya sanar da ofishin jakadancin Birtaniya cewa yaron da aka kama su da shi, zai ba da gudunmowar koda ga ‘yarsa.

“Ike Ekweremadu ya sanar da ofishin jakadancin Birtaniya kan wannan tafiya da zai yi da wannan yaro. Saboda haka, ina goyon bayan Ike.”

XS
SM
MD
LG