Kwamandan rundunar sojojin Amurka a Afirka yace ma’aikatar tsaro ta Pentagon tana fadada ayyukanta a nahiyar a yayin da ake samun karuwar barazanar ta’addanci a nahiyar.
Janar Carter Ham ya fadawa shugabannin sojojin kasashen Afirka jiya litinin a nan Washington cewa uku daga cikin kungiyoyin ta’addanci mafiya hatsari a Afirka, al-Shabab da Boko Haram da kuma al-Qa’ida ta yankin Maghreb, su na kokarin hada hancin ayyukansu wuri guda.
Janar Ham yace kwamandojin Amurka sun samu bayanan dake nuna cewa kungiyoyi uku su na tallafawa junansu da kudi da kuma horaswa kan yadda ake yin amfani da bama-bamai. Ya bayyana lamarin a zaman matsala ga Amurka da kuma batun tsaro a nahiyar Afirka.
Janar din yace ma’aikatar tsaron Amurka tana kokarin fadada ayyukan leken asiri da horaswar soja a Afirka, amma yace sai idan kasashen nahiyar sun gayyaci Amurka ne kawai zata iya yin hakan.
A yanzu dai Amurka tana da sansanin soja na dindin kwaya daya ne tak a nahiyar Afirka a kasar Djib