PDP ta maka gwamnatin jihar Neja kotu saboda daga lokacin zaben kananan hukumomi har sai shekara mai zuwa.
A wani taron da jam'iyyar ta gudanar mataimakin shugabanta na jihar Neja Barrister Tanko Beji ya ce sun je kotun ne domin nuna rashin gamsuwarsu da daga lokacin zaben.
Yace sun kai magana kotu kuma zasu bi su tabbatar cewa an yi abun da yakamata a yi saboda yaudara da hukumar zaben jihar ke yi masu.
To saidai kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa a jihar sun kira taron manema labarai domin nuna goyon bayansu da dage lokacin zaben. Alhaji Isa Ndamaka shugaban kungiyar jam'iyyun siyasa a jihar yace su sun amince saboda dalilai masu karfi da suke da alaka da rashin kudi.
Shi ma gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello a firar da ya yi da manema labarai yace daga lokacin zaben nada alaka da rashin kayan aiki sanadiyar karancin kudi.
A wani lamari kuma majalisar dokokin jihar ta yi zaman gaggawa inda ta bukaci gwamnan ya cire sakataren yada labaransa Dr. Ibrahim Doba wanda majalisar ta zarga da rashin gaskiya..
Ga karin bayani.