Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP-Sabuwa ta Kulla Yarjejeniyar Yin Aiki Tare da APC


Hotunan Babbban Taron Jam'iyyar PDP a Abuja
Hotunan Babbban Taron Jam'iyyar PDP a Abuja

Yarjejeniyar ta tanadi yin aiki tare a tsakanin gwamnonin PDP-Sabuwa da jam'iyyar APC, amma ba ta ayyana cewa gwamnonin sun koma cikin jam'iyyar hamayyar baki daya ba.

A wani matakin dake nuna cewa da alamun jam'iyyar PDP-Tsohuwa da PDP-Sabuwa sun raba gari na har abada, gwamnonin dake karkashin sabuwar bangaren jam'iyyar sun bayyana kulla yarjejeniyar yin aiki tare da babbar jam'iyyar hamayya ta APC.

Wannan sanarwa ta biyo bayan ganawar da sassan biyu suka yi a masaukin gwamnatin Jihar Kano dake Abuja.

Koda yake sanarwar ba ta yi nuni da cewa gwamnonin na PDP-Sabuwa sun koma cikin jam'iyyar APC kacokam ba, da alamun wannan matakin, raba hanya ce baki daya da jam'iyyar PDP-Tsohuwa dake karkashin jagorancin Bamanga Tukur da shugaba Goodluck Jonathan.

Sanata Hadi Sirika, yace matakan nuna kama-karya da cin zarafin da ake yi ma gwamnoni 7 na PDP da suka nuna rashin jin dadinsu da wasu abubuwan da suke faruwa cikin jam'iyyar tasu, da kuma mayarda su 'yan adawa na karfi da yaji, su suka janyo hakan.

Sanata Sirika yace karfin masu hamayya a Najeriya a wannan lokacin, ya shige gaban barazana. Ya ce, tura ta kai mutane bango ne, shi yasa ake ganin irin wannan wutar sauyi na kunnuwa a Najeriya.

Mai ba shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak, yace ai ba wai shugaban ba ya son zama ya tattauna da gwamnonin 7 ba ne, tafiyar da yayi ta sa bai samu zama ya tattauna da su ba. Haka kuma ya musanta cewa gwamnati tana amfani da hukumomi irinsu EFCC wajen cin zarafin masu korafin.

Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko mana da karin bayani.

Sabon kawancen APC Da PDP-Sabuwa - 2:29
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG