A cewar darektan hulda da ‘yan jaridu na kyamfe din gwamna mai jiran gado a Jihar Filato Simon Lalung, Barrister Festus da takardunsa sun garzaya kotu suna bukatar kotun ta dakatar da gwamnati mai ci daga karbar bashin nera biliyan 30.
“Gidajen gwamnati dake unguwar Gwarinpa a Abuja, akwai gidaje 10 hawan sama, muka samu labarin cewa an fara sayar da su, muka yi bincike muka tarar guda biyu an riga an sayar”, a cewar Barrista Festus.
Festus ya kara da cewa “sannan kuma gidan gwamnati sabon da aka gina a Jos, mun samu labarin cewa kayan ciki ana ta fitar da su, ana cirewa wasu kayan da aka sa a wannan gidajen.
Kwamishinan yada labarai a Jihar Alhaji Abubakar Muhammad Badu, yace zargin da gwamnati mai jira take yi ba gaskiya bane.
“Na farko, a bi a hankali. Duk abinda za’a yi, za’ayi wa Jihar Filato ne. Idan gwamnan yana so ya saci kayan gidan, meyasa ya gina gidan?” a cewar Mr. Badu.
A halin da ake ciki kuma, dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a Jihar Filaton Sanata Gyang ya shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zabe inda yake kalubalantar hukumar zabe kan furucinta, na gabatar da Simon Lalung a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.