WASHINGTON, DC —
Kamar yadda masu hikimar magana ke cewa ana magani kai na k'aba, al'amarin jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya sai kara tabarbarewa yake yi a yayin da baraka ke dada yin fadi tsakanin masu yin mubayi'a ga Bamanga Tukur ko Abubakar Kawu Baraje. Duka wannan kuwa na faruwa ne a daidai lokacin da masu sauran kwarin guiwa a jam'iyar ta PDP ke ci gaba da kumajin neman dinke baraka da sasanta tsakani, kamar yadda za ku ji a cikin wannan rahoto d Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko ma na daga Abuja.
PDP Mai Mulkin Najeriya Na Kara Fama da B'araka

Rikicin jam'iyar PDP mai mulkin Najeriya na dada ta'azzara a lokacin da ake kokarin yin sulhu da daidaita tsakani